Download PDF
Back to stories list

Kaza da shanshani Chicken and Millipede

Written by Winny Asara

Illustrated by Magriet Brink

Language Hausa

Level Level 3

Narrate full story The audio for this story is currently not available.


Kaza da shanshani abokai ne. Amma kullum suna takara tsakaninsu. Wata rana, sai suka yi niyyar wasan ƙwallon ƙafa don sanin wa ya fi kwaninta tsakani su biyu.

Chicken and Millipede were friends. But they were always competing with each other. One day they decided to play football to see who the best player was.


Sai suka shiga filin ƙwallon ƙafar kuma suka fara wasan. Kaza tana da gaugawa amma shanshani ta fi ta gaugawar. Kaza ta harba ƙwallon nesa amma kuma shanshani tana aika ƙwallon nesa ƙwarai fiye inda na kazar zai je. Ganin haka, sai da kaza ta fara hassala.

They went to the football field and started their game. Chicken was fast, but Millipede was faster. Chicken kicked far, but Millipede kicked further. Chicken started to feel grumpy.


Ƴan takarar biyu sun yi niyyar su je bugun da kai sai mai tsoron gida. Da farko shanshani ita ce mai tsaron gida wato gola kenan. Kaza ta saka ƙwallo ɗaya rak cikin raga. Sai aka juya, kaza ta zama ma gola mai tsaron gida.

They decided to play a penalty shoot-out. First Millipede was goal keeper. Chicken scored only one goal. Then it was the chicken’s turn to defend the goal.


Shanshani ta harba ƙwallo, kuma ta saka a raga. Shanshani tana gwaninta kuma tana saka ƙwallon. Shanshani ta saka ƙwallon har da kai. Shanshani ta saka ƙwallon biyar.

Millipede kicked the ball and scored. Millipede dribbled the ball and scored. Millipede headed the ball and scored. Millipede scored five goals.


Kaza ta hassala da rishin nasarar da ta yi. Kaza ba ta iya wasa ba. Shanshani ta yi ta dariya saboba abokiyarta ta hassala wajen wasa.

Chicken was furious that she lost. She was a very bad loser. Millipede started laughing because his friend was making such a fuss.


Sai kaza ta buɗe babban bakinta ta haɗiye shanshanin.

Chicken was so angry that she opened her beak wide and swallowed the millipede.


Lokacin da kaza tana shigowa gida, sai ta gamu da uwar shanshani. Sai ta ce mata, “ba ki ga ɗiyata ba?” Kaza ba ta amsa mata ba. Uwar shanshani ta damu.

As Chicken was walking home, she met Mother Millipede. Mother Millipede asked, “Have you seen my child?” Chicken didn’t say anything. Mother Millipede was worried.


Sai uwar shanshani take ji wata ƙaramar murya tana cewa: “Ki agaje ni uwata!” Shanshani take faɗi. Uwar shanshani ta dubu kewayenta da kyau. Muryar nan da cikin kaza ta fito.

Then Mother Millipede heard a tiny voice. “Help me mom!” cried the voice. Mother Millipede looked around and listened carefully. The voice came from inside the chicken.


Uwar shanshanin ta yi ihu “Ki yi amfani da duk azirinki ɗiyata!” Shanshani ta saki wani wari. Sai kaza ta fara jin wani ciwon ciki.

Mother Millipede shouted, “Use your special power my child!” Millipedes can make a bad smell and a terrible taste. Chicken began to feel ill.


Kaza ta yi gyatsa. Kuma ta yi kaki. Ta yi attishewa kuma take ta tari, take tari. Shanshani bai ciyuwa!

Chicken burped. Then she swallowed and spat. Then she sneezed and coughed. And coughed. The millipede was disgusting!


Kaza ta yi ta tari sai ta kako shanshanin da yake cikin cikinta. Shanshanin da uwar sun tafi sun ɓoye cikin wani icce.

Chicken coughed until she coughed out the millipede that was in her stomach. Mother Millipede and her child crawled up a tree to hide.


Tun daka shi kaza da shanshani ba su shiri.

From that time, chickens and millipedes were enemies.


Written by: Winny Asara
Illustrated by: Magriet Brink
Language: Hausa
Level: Level 3
Source: Chicken and Millipede from African Storybook
Creative Commons License
This work is licensed under a Creative Commons Attribution 3.0 International License.
Options
Back to stories list Download PDF