Download PDF
Back to stories list

Mi ƙanwar Idi zata ce? What Vusi's sister said

Written by Nina Orange

Illustrated by Wiehan de Jager

Language Hausa

Level Level 4

Narrate full story The audio for this story is currently not available.


Wata rana da farar safiya, kakar Idi ta yi kiran shi, “Idi, don Allah, kana iya kai ma mahaifanka wannan ƙwan? Suna son su yi wani babban biskiti na auren ƙanwarka”.

Early one morning Vusi’s granny called him, “Vusi, please take this egg to your parents. They want to make a large cake for your sister’s wedding.”


Lokacin da yake zuwa gida mahaifan nashi, Idi ya gamu da wasu samari biyu suna cirar ƴaƴan itace. Ɗaya daga cikin yaran ya ɗauki ƙwai ɗaya kuma ya jefa saman iccen. Ƙwan ya fashe.

On his way to his parents, Vusi met two boys picking fruit. One boy grabbed the egg from Vusi and shot it at a tree. The egg broke.


“Mi ka yi?” in ji Idi. “Wannan ƙwan na yin biskiti ne, biskitin auren ƙanwata. Mi ƙanwar tawa za ta ce idan babu biskitin aurenta?”

“What have you done?” cried Vusi. “That egg was for a cake. The cake was for my sister’s wedding. What will my sister say if there is no wedding cake?”


Samari ba su ji daɗin wannan wasan da suka yi ma Idi. “Babu yadda zamu yi don yin biskiti, amma ga wannan sandar ka kai ma ƙanwarka.” In ji ɗaya daga cikin su. Idi ya ci gaba bisan hanyarshi.

The boys were sorry for teasing Vusi. “We can’t help with the cake, but here is a walking stick for your sister,” said one. Vusi continued on his journey.


Bisan hanya, ya tarda mutane biyu suna gina wani gida. “Muna iya amfani da wannan sandar taka mai ƙwari?” in ji ɗaya daga cikin mutanen biyu. Amma da yake sandar ba ta da ƙwari sosai, sai ta kariye.

Along the way he met two men building a house. “Can we use that strong stick?” asked one. But the stick was not strong enough for building, and it broke.


“Mi kuka yi?” in ji Idi. “Wannan sandar kyauta ce aka ma ƙanwata. Masu ciran ɗiyan itace suka ba ni don sun fasa ƙwan da za yi biskitin auren ƙanwata. Biskitin na auren ƙanwata ne. Yanzu ba ƙwan, ba biskitin kuma babu kyauta ko ɗaya.” Mi ƙanwar tawa za ta ce.

“What have you done?” cried Vusi. “That stick was a gift for my sister. The fruit pickers gave me the stick because they broke the egg for the cake. The cake was for my sister’s wedding. Now there is no egg, no cake, and no gift. What will my sister say?”


Maginan ba su ji daɗi ba da suka karya sandar. “Ba mu san abinda za mu yi ba, amma ga ciyawa kaɗan ka kai ma ƙanwarka,” in ji ɗaya daga cikinsu. Idi ya ci gaba bisan hanyarshi.

The builders were sorry for breaking the stick. “We can’t help with the cake, but here is some thatch for your sister,” said one. And so Vusi continued on his journey.


Bisan hanya, Idi ya tarda wani makiyayi da saniya. “Wannan ciyawar sai ta yi daɗi, ko ka ba ni kaɗan?” in ji saniyar. Sai da yake ciyawar tana da daɗi, saniyar ta cinye duka.

Along the way, Vusi met a farmer and a cow. “What delicious thatch, can I have a nibble?” asked the cow. But the thatch was so tasty that the cow ate it all!


“Mi kika yi?” in ji Idi. “Wannan ciyawar, kyauta ce aka ma ƙanwata. Magina sun ba ni ciyawar don su karya sandar cirar ɗiyan itace. Masu cirar ɗiyan itace sun ba ni sandar don sun fasa ƙwan yin biskitin auren ƙanwar tawa. Biskitin na auren ƙanwata ne. Yanzu babu biskitin, ba kuma kyauta ko ɗaya. Mi ƙanwar tawa za ta ce?”

“What have you done?” cried Vusi. “That thatch was a gift for my sister. The builders gave me the thatch because they broke the stick from the fruit pickers. The fruit pickers gave me the stick because they broke the egg for my sister’s cake. The cake was for my sister’s wedding. Now there is no egg, no cake, and no gift. What will my sister say?”


Saniya ba ta ji daɗi ba da ta cinye ciyawar. Makiyayin ya ɗauki niyyar bada saniya don ta raka shi kuma ta zama kyauta ga ƙwanwarshi. Idi ya ci gaba bisan hanyarshi.

The cow was sorry she was greedy. The farmer agreed that the cow could go with Vusi as a gift for his sister. And so Vusi carried on.


Sai dai lokacin da za a yanka saniyar, sai ta gudu ta koma ga mai ita. Idi kuma ya ɓadda sawunta. Ko da ya zo wajen auren ƙanwar tashi, mutane sun yi abinci.

But the cow ran back to the farmer at supper time. And Vusi got lost on his journey. He arrived very late for his sister’s wedding. The guests were already eating.


“Mi za ni yi ?” in ji Idi. “Saniyar da ta gudu, kyauta ce kambacin ciyawar da magina suka ba ni. Magina sun ba ni ciyawar don sun karya sandar cirar ɗiyan itace. Masu cirar ɗiyan itace sun ba ni sandar don sun fasa ƙwan yin biskitin auren ƙanwar tawa. Biskitin na auren ƙanwata ne. Yanzu babu saniyar, ba biskitin, ba kuma kyauta ko ɗaya.”

“What shall I do?” cried Vusi. “The cow that ran away was a gift, in return for the thatch the builders gave me. The builders gave me the thatch because they broke the stick from the fruit pickers. The fruit pickers gave me the stick because they broke the egg for the cake. The cake was for the wedding. Now there is no egg, no cake, and no gift.”


Ƙanwar ta Idi ta yi tunani kuma ta ce: “Idi ƙanena, ban damu da wannan kyautar. Ban damu da biskitin ba. Yau ranar murna ce, ina farin ciki. Sanya tufafinka na salla ka zo mu raya wannan ranar!” Sai idi ya yi hakan.

Vusi’s sister thought for a while, then she said, “Vusi my brother, I don’t really care about gifts. I don’t even care about the cake! We are all here together, I am happy. Now put on your smart clothes and let’s celebrate this day!” And so that’s what Vusi did.


Written by: Nina Orange
Illustrated by: Wiehan de Jager
Language: Hausa
Level: Level 4
Source: What Vusi's sister said from African Storybook
Creative Commons License
This work is licensed under a Creative Commons Attribution 3.0 International License.
Read more level 4 stories:
Options
Back to stories list Download PDF